Kamfanin dilancin labaran Najeriya ya rawaito cewa jami’an tsaro sun hana mahalarta taron da 'yan jaridu shiga fillin da aka shirya taron.
Manema labarai a yankin sun rawaito kakkakin ‘yan sanda jihar ta Rivers, Nnamdi Omoni na tabbatar da haka tare da cewa sunyi hakan ne bisa umarni kotu.
A jiya ne dai babbar kotun Abuja ta haramta gudanar da taron, wanda kuma ke zuwa bayan da wata babbar kotun Fatakwal ta bayar da umarnin a yi taron.
kafin hakan dai an yi tsammanin daidaita bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Jam'iyyar wato Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi a taron.288